1 of 3Classic · 3 chapters

This film is a perfect introduction to Jesus through the Gospel of Luke. Jesus constantly surprises and confounds people, from His miraculous birth to His rise from the grave. Follow His life through excerpts from the Book of Luke, all the miracles, the teachings, and the passion. God creates everything and loves mankind. But mankind disobeys God. God and mankind are separated, but God loves mankind so much, He arranges redemption for mankind. He sends his Son Jesus to be a perfect sacrifice to make amends for us. Before Jesus arrives, God prepares mankind. Prophets speak of the birth, the life, and the death of Jesus. Jesus attracts attention. He teaches in parables no one really understands, gives sight to the blind, and helps those who no one sees as worth helping. He scares the Jewish leaders, they see him as a threat. So they arrange, through Judas the traitor and their Roman oppressors, for the crucifixion of Jesus. They think the matter is settled. But the women who serve Jesus discover an empty tomb. The disciples panic. When Jesus appears, they doubt He's real. But it's what He proclaimed all along: He is their perfect sacrifice, their Savior, victor over death. He ascends to heaven, telling His followers to tell others about Him and His teachings.

Ask yours

Bible Quotes

Share
Free Resources

Want to understand the Bible more deeply?

Join our Bible study

Transcript

Hausa ( حَوْسَ)
Allah mai girma shine me iko mafi daraja Sammai na faɗin girman sa tsararraki na bayyana aikin hannuwan sa Kullu yaumin suna maganar sa dare da rana suna shedar sa Sa'adda Allah ke halittan sammai. Ya kuma halicci duniya sai ya siffanta mutum daga turɓayar ƙasa. Ya hura masa numfashi Allah mai ƙauna ya halicci maniji da mace acikin siffar sa domin suyi dangantaka da shi. Da farko haka kuwa suka girmama Allah suka ɗaukaka shi suka yi rayuwar da ta dace tare. Haka ya cigaba har sai ranar da sheɗan ya jarabci macen ta tsinka daga ƴaƴan itacen da aka hana su ci. Ta koshi ta kuma baiwa mijin ta shi kuma ya ci. Yin hakan kuwa ya zama sanadin tawaye da bin nufin kan mutum. Ta dalilin zunubin nan ne mutum ya rabu da Allah, Allah kuwa ya kore shi daga gonar adinin. Amma duk da haka Allah ya ƙaunaci ɗan Adam. Ba son sa bane ya rabu da halittar sa. Amma kuwa tayaya Allah mai tsarki mai adalci zai kasa sharhanta zunubin ɗan Adam. A cikin littafi mai tsarki Allah ya bayyana shirin da ya yi na ceton duniya da yayi daga shari'ar sa. Annabi Ibrahim ne na farko da aka nuna masa wannan shirin. Mutum ne mai adalci da Allah ya yi aiƙawari zai albarkace shi zai ruɓaɓɓaya zuriyar sa kaman taurari da yashi a gaɓar teku. Allah ya gwada biyayyar Ibrahim da ya umurce shi ya yi hadaya da ɗan sa. Ya dogara ga Allah ya yi biyayya da shi. Da Ibrahim ya ɗaga wuƙar ya yanka ɗan sa sai mala'ikan Allah ya tsaida shi. Ya san shi mai tsoron Allah ne mai biyayya. Sai Ibrahim ya ga rago da ƙahonni a sarƙafe cikin kurmi. Ya kama ya yi hadaya a maimakon ɗan sa. Ta haka ne Allah ya nuna wa Ibrahim cewa dole ne a yanka rago ko wata dabba makamanciya. Don shafe zunubban mutum har sai Allah ya kawo cikakkiyar hadaya domin fansar zunubai. Maimakon zunubi ya raba mutum da Allah hadayar zata maida dangantakan su. Littafi mai tsarki na cewa akwai wanda zai zo, zai zama cikakkiyar hadaya domin zunuban mutum. Yanda rago ya ɗauki matsayin ɗan Ibrahim haka mai zuwan zai maye gurbin mutum don samun gafara. Wasu nace da wannan mai zuwa almasihu. Wato wanda zai zo ya sulhunta duniya da Allah. Annabawa sunyi annabcin abubuwa na musamman game da almasihu kafin yazo. Annabi Ishaya yace haihuwar sa zata zama abar al'ajabi. Budurwa za tayi juna biyu ta haifi ɗa za'a ce da shi ɗan Allah wato aruhu bata jiki ba. Annabi Mika ya shaida za'a haifi Almasihu a baitallami. Annabi Zakariya ya yi annabci sai shiga birnin Urshalima bisa kan jaki. Yahuza ɗaya daga cikin mabiyansa zai bashe shi. Annabi Ishaya yace shafaffafe na Allah zai kawo labari mai daɗi ga talakawa. Ze warkar da masu karaya a zuciyan shi ya kwance ɗ`aurarru. Cewa lokaci yayi da ubangiji zai ceci mutanen sa. Wanene almasihu? Anyi annabi mai suna Yesu. Wasu sun zaci shine annabawa su kayi zancen sa, ko haka ne? Ko rayuwar su ta cika annabcin? Ko yesu yafi matsayin annabi? Abinda zakaji yanzu labarin yesu ne bisaga shaidun. Acikin littafi mai tsarki. Wannan kwaikoyo wani ya cike gurbin Yesu. Koda yake babu mutumin da ya isa. Anyi wannan shiri ne domin mu gane mu kuma anfana ta rayuwar Yesu. Ina rubuta maka ya Tiyofalas. Al'amuran da suka tabbata a wurin mu. Don kasan ingancin maganar da aka sanar da kai Azamanin da Kaisar Augustus yana mulkin Roma Da kuma Hirdus sarkin Yahudiya Allah ya aiko malaika Jibirulu wani gari mai suna Nazaret Gun wata budurwa, Maryamu Kadda ki ji tsoro Maryamu Kin sami tagomashi gun Allah Zakiyi ciki Ki haifi Da ki sa masa Suna Yesu. Ƙaƙa wannan zai yuwa? Da shike ni budurwa ce? Ruhu mai tsarki zai sauko maki, Don haka Mai tsarkin nan da zaki haifa Za'a ƙirashi ɗan Allah Mulkin sa Babu ma tuƙa Sai Maryamu ta tafi kasar Yahudiya Don ta gaida Alisabatu yar'uwanta Wadda ta ke da juna biyu. Alisabatu Maryamu Ƴar'uwata Ke mai albarka ce a cikin mata Ɗan cikin ki ma mai albarka Danaji gaisuwarki Jaririn da ke ciki na ya motsa da farin ciki Zuciyata na daukaka Ubangiji Ruhuna kuma na farin ciki da Ubangiji mai ceto na Yanzu tsararraki zasu ƙira ni mai albarka Yaku mutanen Nazaret Kaisar Augustus ya yi shelar cewa A rubuta sunayen da ke zaune ƙasar Yahudiya Kowa ya tafi a rubuta shi A jihar sa Da garinsa na asali Yusufu da Maryamu sun je Baitalami ta Yahudiya don a rubuta su Amma basu sami masauƙi a Urshalima ba Sai suka sauƙa a ɗakin tumaki Ayankin ƙasar Wasu makiya na tsaron garken su da daddare Sai ga mala'ikan Ubangiji kusa da su Hasken Ubangiji ya haskaka su Yau a birnin Dauda an haifa mu ku mai ceto Shine Almahisu Makiyayan suka tafi da sauri Su ga jaririn ƙwance a kwami Su suka fara kai labarin nan mai daɗi na haihuwar Mai ceto Da rana ta takwas tayi da za'ayi masa kaciya Aka sa mai suna Yesu Yusufu da Maryamu suka kai shi Urshalima su miƙa shi ga Ubangiji. A Haikalin akwai wani adali mai suna Samilu Ruhu ya nuna masa bazai mutu ba sai ya ga Almasihu Ya Allah Yanzu ka sallami bawanka lafiya Bisa ga maganar ka Yanzu naga ceton ka zahiri Yaron nan zaɓaɓɓen Allah ne Allah ya albarkaceku Bayan wasu watanni sai Yusufa da iyalin sa suka koma gidan su a Nazaret. Alokacin da Yesu keda shekara goma sha biyu Yusufu da Maryamu suka kaishi Urushalima don idin Faska Amma alokacin da suke komawa gida a tsammamin su yaron yana tare da su Ashe Yesu ya tsaya a baya Sai suka koma birni suna ta neman sa A rana ta uku suka same shi a haikali zaune tare da manyan malamai da dattiɓai. Shin ɗan wanene ke tambayoyi haka? Daga Nazaret ne Mun zaci yana bin mu Ku gafarce shi Masu jin sa sunyi mamaki Ɗana... Yaya kayi mana haka? Ni da baban ka muna ta neman ka duk ran mu a ɓace Meyasa kuke nema na bakusan wajibi ne inyi sha'anin ubana ba? Ya koma Nazeret da su Ya ƙaru da hikima da girma da tagomashi gun Allah da mutane A shekara ta sha biyar na mulkin Kaisar Tubariyas Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya Hirdus yana sarautar Galili Hanana da Kayafas ne manyan Firistocin Maganar Allah ta zowa Yahaya a jeji Yabi lardin kogin Urdun Yana wa'azi mutane su tuba a gafarta zunubansu Ku juyo daga zunubanku Ayi maku babtisma Allah zai gafarta maku Yadda yake rubuce a littafin Annabi Ishaya Murya na kira a jeji cewa Ku shirya ta farkin Ubangiji Ku miƙe hanyoyin da zaibi Za'a cike ko wani kwari Kowani dutse da tsauni za'a baje su Za'a miƙe karkatattun wurare Da gyara munanan hanyoyi Dukkan ƴan adam Za suga ceton Allah Me zamuyi? Gaya mana? Me zamu yi? Ku mugayen macizai Me ka keso muyi? Taimake mu Gaya mana hanyar da zamubi? Wanda yake da taguwa Biyu Yaraba da wani Mara Ita Duk mai abinci kuma Ya raba da wasu Malam Mu masu karɓan haraji ne Me zamu yi? Kar ku karɓi fiye da abunda aka umurce ku Amma mufa? Me zamuyi? Kada ku kwacema kowa kudi Da ƙarfi Kada kuma ku zargi wani da karya Kudai dangana da albashin ku Gaya mana kai ne Almasihu? Ni ina maku babtisma da ruwa Amma wani na zuwa ya fini girma sosai Ko takalminsa ma ban isa in kwance ba Zaiyi muku babtisma da ruhu da kuma wuta Ƙwaryar shiƘarsa na hannun sa Ya share masussuka ya tara alkama Yasa a rumbun sa Ruhu mai tsarki ya sauƙo bisansa da kamannin kurciya Murya daga sama tace Kai ne ƙaunataccen ɗana ina murna da kai Da Yesu ya fara koyarwa yana da shekara talatin Ya dawo daga kogin Urdun cike da ruhu mai tsarki Ruhu ya izashi jeji har kwana arba'in, Ibilis na gwada shi a kwanakin bai ci komai ba Sai Ibilis yace masa In kai ɗan Allah ne ka umurci dutsen nan ya zama gurasa An rubuta Bada gurasa mutum zai rayu ba sai da maganar Allah Sai Ibilis ya kaishi wani wuri ya nuna masa dukkan mulkokin duniya Zan baka dukkan wannan iko da daukakar su Don ni aka baiwa Na kan iya bawa duk wanda naga dama In zaka yi mini sujada An rubuta kayiwa Allah ka sujada Shi kaɗai zaka bauta wa Sai Ibilis ya kaishi Urshalima kuma Ya ɗora shi kan tsororuwar haikali In kai dan Allah ne ka dira kasa daga nan don an rubuta cewa zai yiwa mala'ikun sa umurni su kiyaye ka, su tallafe ka don kada kayi tuntube da dutsen Nassi yace Bazaka gwada Ubangiji Allahn ka ba Yesu yazo Nazarat inda aka reneshi Sannu ƴata, Sannu Ya shiga haikali ran asabar kamar yadda ya saba Aka miƙa masa littafin annabi Ishaya Ruhun Ubangiji yana tare da ni Domin ya shafe ni in yiwa matalauta bishara Ya aiko ni inyi shela saki ga daurarru in kuma bude wa makafi ido In yantar da waɗanda aka danne su In sanar lokacin Ubangiji yayi na ceton mutanen sa Umm...gaskiyar ka Gaskiyar wannan nafsi ta cika yau Kamar yadda ku kaji Wannan nafsi ya cika? Masihu ne kadai zai iya cika wannan alkawarin. Yaya zamu sani? Masu shakka kun yi mini karin magana Likita warkar da kanka Zaku kuma cemini Duk abinda munji kayi a Kapernahum Kayi a nan garin ku Ina kaya maku Annabi baya karuwa a garin sa Da kalmonin nan Yesu ya bayyana kansa Shi ne Almasihu shafaffe da aka aiko ya ceci mutanen sa Amma Yahudawa sun ƙi shi Sun so su jefar da shi ƙasa Amma ya ratsa tsakiyar su Ya yi tafiyarsa Ya nufi wajen Kapernahum a kasar Galili Al'ummar Romawa ke musu mulkin mallaka Jama'a kuwa na marmarin zuwan shafaffe na Allah don ya cecesu Salama gareku Yawwa Barka Jirgin ka zai ɗauken Siman? Me zai hana Bazai tafi ba ko? Yi mana magana Yi mana magana Yi magana da mu Yesu Wasu mutum biyu sun shiga Haikali yin addu'a Bafarise da kuma mai karɓar haraji Bafarisen ya miƙe yin addu'a ya ce Ya Allah nagode da yake ni ba kamar sauran mutane nake ba, mazambata, marasa adalci, mazinata ko kamar mai karɓan harajin nan A mako ina azumi sau biyu Komi na samu nakan fitar da zakka Mai karbar haraji kuwa ya na tsaye nesa Bai ɗaga kai sama ba Ya bugi ƙirjin sa yace Ya Allah Kaji tausayina mai zunubi Kuji Mai karɓan haraji ya koma gidan sa baratacce Ba kamar ɗayan ba Duk mai ɗaukaka kan sa ƙasƙantar da shi za'ayi Mai ƙasƙantar da kansa kuwa Ɗaukaka shi za'ayi Yi gaba da jirgi zuwa gu mai zurfi Ku saki tarko ku zanyo kifi Maigida munyi fama dukkan dare Amma bamu kama komai ba Amma tunda kace haka Za mu jefa tarunan Yakubu, Yahaya Yakubu, Yahaya ku kawo jirgin ku da sauri ku taimaka mana Baza mu iya ba Muna da abunyi Madallah Madallah Rabu da ni ya Ubangiji Ni mai zunubi ne Kada kuji tsoro Yanzu mutane zaku rinka kamowa Kuzo gareni ku ji magana ta Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa Ku kira gareshi tun yana kusa Masu mugunta su bar al'amuran su Su juyo ga Ubangiji gama shi ne mai jin ƙai Mai saurin gafartawa Kuyi gaskiya da adalci Zaku kuwa bayyana adalcin sa Za'abi da ku da salama Yana zuwa Gashi nan Yesu Yesu In ka yarda ka ceci ƴata tilo Yi mana jinkai Shekarunta sha biyu tana bakin mutuwa in ka yarda kazo muje Ayya Yairus Yesu Ƴar ka ta rasu kar ka wahalar da Malamin Kada kaji tsoro Kaba da gaskiya zata warke Ku daina kuka Bata mutu ba Barci takeyi Ɗiya Tashi A bata abinci taci Na umurceku Kar ku faɗawa kowa wannan Bayan haka sai ya ga wani mai suna Lawi dab da ƙofar gari yana karban haraji Biyoni Yesu ya hau dutse yin addu'a dukkan dare yana addu'a ga Allah Da gari ya waye ya gaida sha biyun da ya zaɓe su manzanni Siman daya bashi suna Bitrus Da ɗan uwansa Andarawus Yakubu Yahaya Filibus Batalamowus Matiyu Toma Yakubu ɗan Halfa Saminu mai suna Zaloti Da Yahaya ɗan Yakubu Da Yahuda Iskariyoti maci amana Albarka ga matalauta Domin mulkin Allah naku ne Albabarka ga ku mayunwata don za'a ƙosar daku Albarka ga masu kuka don zasu yi dariya Masu albarka ne da mutane suka ƙi ku suka zargeku, suka yi kyamar sunan ku saboda ɗan mutum Kuyi murna da tsalle a wannan rana Domin ladar ku me yawa ce a sama Haka ma kakannin su suka yiwa annabawa Sha shida, sha bakwai, sha takwas, sha tara, ashirin Iyakar kenan Wa yace iyakar kenan? Kaiton ku masu arziki yanzu Kun samu taku ta'aziyyar [Dariya......] Baya son arziki Ai ya haukace Kiton ku masu dariya yanzu Zaku yi kuka da baƙin ciki Kaiton ku in kowa na yabon ku Haka kakannin su suka yiwa annabawan ƙarya Ina gaya maku masu sauraro ku kaunaci magabtanku Yiwa maƙiyan ku alheri Albarkacin masu zargin ku Yima masu walaƙanta ku addu'a In wani ya mareka a ɗayan kunci Juya masa ɗayan kuncin ma In ya kwace mayafin ka Ka bashi taguwarka ma Kaba duk wanda ya roƙe ka In kuma an kwace kayan ka Kada ka nemeshi Kuma yiwa mutane yadda kuke so suma suyi maku In masoyanku kawai kuke kauna Wace lada ku ke da ita Ko masu zunubi na ƙaunar masu ƙaunar su In mai alheri kuke yiwa alheri Wace lada ce gareku Haka masu zunubi suke yi Ya ya zai taba ta, Yaya zai yi magana da ita Abin ƙyama A'a Ku ƙaunaci magabtanku Kuyi masu alheri Ku bada rance banda tsammanin biya Ladar ku mai yawa ce Zaku zama 'ya'yan Allah mai girma Shi me alheri ne ga masu butulci da mugaye Ku tausaya Yadda ubanku ke tausayawa Yesu ka cecemu Kada ku bada laifi don kar a baku Kada ku hukunta Don kada ayi maku haka Ku yafe Kuma za'a yafe maku, Kafishemu ya Ubangiji Ku bayar Kuma sai a baku Mudun da ku ke aunawa da shi za'a auna maku Makaho Ba ya yiwa makaho jagora Ai dukan su biyu sai su fada a rami Don me ka ke duban haki a idon wani baka kula da gungumen da ke a naka ba? Ubangiji ka fishe mu Muna bukatarka yanzu Ubangiji Mai murna ce mahaifiyar ka da kasha mamanta Albarka ta tabbata ga masu jin maganar Allah Suna kiyayewa Ina so in san mutumin nan Kana zato shi ne Almasihu Bafarise ya gayyacesu cin abinci a gidan sa Yesu kuwa yaje garin ya zauna ya ci Yara ku tafi kunji ko Kunji ni tafi Sun iya yin kowace irin fitina Me ta keyi haka ban sani ba Me ta keyi Da shi annabi ne da yasan kowace irin macece ke taɓa shi Da yasan cewa ita mai zunubi ce Nasan kowace irin macece Saminu Saurara kaji Akwai wani mai bin mutum biyu bashi Ɗaya tsabar kudi ɗari biyar ɗaya kuma hamsin Da suka kasa biya Sai mutumin ya yafe musu dukansu biyu Wa zai fi kaunarsa acikin su? Agani na wanda aka yafewa mai yawa Dai-dai ne Ka ga matannan Nazo baka bani ruwan wanke ƙafa ba Amma ta wanke ƙafafuna da hawayen ta Ta goge da gashin kanta Kai baka sumbanceni ba Tun shigarta bata daina sumbartan ƙafafuna ba Baka shafa mani mai a kai ba Ita ta shafa min man ƙamshi a ƙafafuna Ina gaya maka Don wannan an gafarta mata zunuban ta duka Wanda an gafartawa kaɗan Ƙauna kaɗan ya keyi An gafarta zunuban ki. (aaah wannan saɓone babban saɓo) Jeki ban gaskiyar ki ta ceceki Bada daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye ya na wa'azi yana yin bisharar Allah Sha biyun nan kuwa suna tare da shi da waɗansu mata da aka raba da baƙaƙen aljanu da kuma rashin lafiyar su Cikin su da Maryamu mai suna Magadariya wadda aka fitarwa da aljanu bakwai Da Yuwana matar Kuza wakilin Hirdus Da Suzanatu da kuma wadansu da yawa da suka yi masu ɗawainiya da kayan su Hirdus sarkin Galili wanda Yahaya ya tsawatawa akan auren matar dan uwansa ya ƙulle Yahaya a kurkuku Lafiya....... da muka kusanci ƙofar gari Na'im Mutane suka fito dauke da gawa Mamacin shi kadai ne ga uwa tasa Da Yesu ya ganta Yaji tausayinta Ya taɓa makarar yace "Saurayi nace maka ka tashi." Mamacin ya tashi ya zauna Yesu ya bada shi ga uwa tasa Tambaye shi kuce Kai ne annabi Ishaya yace ke zuwa? Ko kuwa musa ido ga wani Megida Megida Yahaya mai babtisma ne ya aiko mu Mu tambaya ko kai ne me zuwan nan Ko musa ido ga wani Gayawa Yahaya abinda kun ji kun gani Makafi na gani Guragu na tafiya Albarka ga wanda baya tuntuɓe domina Ɗora ni a kafaɗar ka Eeh Ina ganin Yesu Eeh inaganin Yesu Wani mai shuka ya tafi shuka Yana watsa iri sai wasu suka faɗa a hanya aka tattake su Tsuntsaye suka tsince irin Wasu suka faɗa a dutsi Da suka tsiro sai tsiron suka bushe saboda babu damshi Wasu kuma suka faɗa a ƙaya Suka tashi tare amma Sai ƙayar ta shake su Wasu suka faɗa a ƙasa mai kyau sunyi girma sunyi tsaba sosai Kamar riɓi ɗari-ɗari Shugaba Don me ka ke magana da misalai duk lokacin taro? Kukam an yardan muku Kusan asirin Allah Amma ga sauran sai da misali don su gani bazasu gane ba Su ji bazasu fahimta ba Ga bayanin wannan misali Irin Maganar Allah ce Waɗanda suka faɗa a hanyan sune masu jin maganar Sai sheɗan ya dauƙe maganar daga zuciyarsu don kada su gaskanta su samu ceto Nakan dutse kuwa da zaran sunji maganar sai su karba da farin ciki Sukam basu da tushe Sukan gaskata kwanaki kaɗan Amma in lokacin gwaji yayi Sai su ridda Wai'nda sun faɗa a cikin ƙaya sune masu jin magana Amma yawan taradadin duniya, dukiya da shagalinta sun shaƙe su Har su kasa yin amfani Waɗanda aka shuka kasa mai kyau Sune wadanda suka ji maganar Suka rike ta kamkam da kyakkyawar zuciya Suku jure har suka yi amfani Ba mai kunna fitila ya rufe ta da masaki Ko yasa a ƙarkashin gado a'a Sai ya dora a madorinta Domin masu shiga suga haskenta Ba abinda ke boye da baza'a bayyana ba Ba kuma asirin da bazai tono ya zama bayyananne ba Ku kulafa ku iya ji Duk mai abu akan ƙarawa Marar abu kuwa ko abinda yake tsammani yake da shi sai a karɓe daga gurin sa Malam mahaifiyar ka da ƴan'uwan ka suna waje suna son ganinka Masu ji suna aikata maganar Allah Sune ƴan'uwana Wata rana Yesu ya shiga jirgin ruwa tare da almajiran sa Yace masu Mu haye wancan hayin teku Suna cikin tafiya sai barci ya kamashi Megida Megida Yesu Hadari zai hallaka mu Zamu nitse Ka cecemu ya Ubangiji Ashe zamu tsira Ina bangaskiyar ku Suka iso ƙasar Garasinawa wanda ke ƙetaren tafkin Galili Yesu dan Allah madaukaki Ina ruwan ka da ni Na roƙeka Karka azabtar da ni Ya ya sunan ka Tuli Ubangiji mun roƙeka Kada ka wahal da mu Bari mu shiga Cikin garken Garken Aladu Kai dawo Tsaya Tsaya Aljanun sun rabu da mutumin sun shiga aladun Tafi daga nan Kai matsafi Rabo damu Tafi daga wurin nan Rabu da mu Tafi daga nan Zan bika duk inda zaka Bari In bika Koma gida Ka faɗi abinda Allah ya yi maka Yesu da almajiransa sun janye jikinsu zuwa Baitasda Amma taron suka gane Sai suka bishi. Chan da rana Bitrus yace Shugaba Ka sallami jama'a su tafi kauyuka da Gonaki su samu abinchi da masauki. Domin nan gurin Bakowa. To ku kubasu abinci mana su ci. Abun da muke dashi kenan gurasa biyar da kifi biyu. Me albarka ne Ubangiji sarkin sarakuna Wanda yake bada abinchi daga ƙasa La abin al'ajabi. Abin mamaki Wa mutane ke cewa nake Wasu sunce Yahya me baptisma ne Wasu kuwa sunce Iliya ne Wasu kuma suna cewa ɗaya daga cikin annabawan da ne Ya tashi da rai To amma kufa Wa kuke cewa nake? Almasihu na Allah Kada ku gayawa kowa wannan Lallai ne dan mutum zaya sha wuya a ƙishi Za'a kashe shi Amma bayan kwana uku zai tashi da rai Akwai wanda zai iya biyo ni? Zan bika shugaba Amma da fari bari inje inyi bankwana da iyalina, Mai huɗa dake yin huɗa yana dubin baya bai dace da mulkin Allah ba Duk mai son ya biyoni kuwa sai yaƙi kansa tukuna Ya ɗauki giciyen sa kowace rana ya biyoni Duk wanda yake son ransa Zai rasa shi Wanda kuma zai bada ransa domina Tattalinsa yake Mai mutum zai amfana in ya samu dukkan duniya ya rasa ransa Wanda ya ji kunyar shaida ni da maganata Ɗan mutum zaiji kunyar shaidarsa in yazo cikin daukakarsa Da daukakar uba da ta mala'iku masu tsarki Ina tabbatar muku Akwai waɗansu anan cikin ku da bazasu mutu ba sai sunga mulkin Allah Yesu ya ɗauki Bitrus da Yahaya da Yakubu ya hau dutse yin addu'a Yana addu'a sai kamanninsa suka sake Tufafin sa kuma suka yi fari fat Sai ga mutum biyu na magana da shi Annabi Musa da Iliya sun bayyana cikin daraja Zaka cika nufin Allah Zaka mutu a Urshalima Annabawan na rabuwa da shi sai Bitrus yace wa Yesu Shugaba Yana da kyau da muke nan Mu kafa bukkoki uku Ɗaya taka Yana magana sai gajimare ya rufe su suka tsorata Sai aka ji muryar zati na cewa Wannan shi ne zaɓaɓɓen ɗana kubishi Malam Malam Ina roƙon ka ka dubi ɗana Kaji juyayin sa Don shi kaɗai ne gareni Na roƙi almajiran ka su fitar da aljannun Amma sun kasa Ya ku tsara marasa ban gaskiya Har yaushe zan zauna ina ta haƙuri da ku? Kawo ɗan ka nan Ya warke fuskarsa tayi haske, abun mamaki Koya mana addu'a wadda Yahaya ya koyawa almajiransa Idan kuna addu'a kuce Ya uba dake cikin sama A tsarkake sunayenka Mulkin ka yazo Mulkin ka ya tabbata a sama da ƙasa Ka bamu abincin yini Ka gafarta mana laifofinmu gama muna gafartawa duk wanda yake mana laifi Kada ka kaimu wajen jaraba Amma ka cecemu daga mugu Ku roƙa za'a baku Ku nema zaku samu Ku ƙwanƙwasa Za'a buɗe maku Wanda ya roƙa akan bashi Mai nema zai samu Wanda ya ƙwanƙwasa kofa za'a buɗe masa Hahaha Wani uban kirki ne acikin ku Zaiba ɗan sa maciji In ya roƙeshi kifi Ko ya bashi kunama in ya roƙeshi kwai Kuda kuke miyagu kun iya ba ƴaƴanku masu kyauta kyau Balle uban ku dake sama, zai bada ruhu mai tsarki ga duk masu rokon sa Ina gaya muku Kada ku damu da ranku don abinda zaku ci Ko kuma jikin ku abinda zaku sa Domin rai yafi abinci Jiki kuma yafi tufafi Kudubi hankaki Basa shuka ka girbi basu da taska ko rumbu Amma Allah na cishe su Saunawa darajarku tafi ta tsuntsaye Wanene acikin ku don damuwa Zai ƙara tsawon ransa? In ba zaka iya abu haka ba Don me kake damuwa dasaura Ku duba furanni Yadda suke girma Basa shuka ko girbi Duk da haka ko adon Sulemanu ma bai kai na ɗayan su ba In Allah Yana lura da tsire-tsiren jeji wanda yau yana raye gobe a jefa a murhu Balle ku yan adam da Allah ya baku daraja Ya ku masu ƙarancin ban gaskiya Ka ƙarfafa bangaskiyar mu Da kuna da bangaskiya kamar ƙwayar munsar Zakuce wa itacen durumin nan Ciruka dasu cikin teku Sai kuwa ya bi umarninku. Dalilan zunubi dole suzo Amma kaiton wanda shine sanadiyar su Gara a ratayawa mutumin nan dutsin niƙa a jefa shi cikin take da yasa daya daga cikin ƴan ƴarannan ya yi lefi Mulkin Allah yana kama da me? Ya na kama da haka Wani mutum ne ya ɗauko kwayar munsar ya shuka a lambun sa Ta girma tayi itace tsutsaye sukayi sheƙar su a rassanta Bangane abunda yake faɗi ba Don me kuke ci kuke sha da masu karɓar haraji da masu zunubi Lafiyayyu ba ruwansu da mai magani sai dai marassa lafiya Banzo kiran masu adalci don su tuba ba Sai masu zunubi Sake gaya mana game da mulkin akwai wani abu kuma? Kada kuji tsoro ƙaramin garke Allah na baku rabo a mulki Ku sayar da mallakarku, kuba matalauta Ku samu ma'ajin da baya ƙarewa Kuyi ajiya a sama Inda ba mai rage ta Inda ba ɓarawo da zai sata Ba'a son da zai taɓa Inda dukiyarka take nan zuciyarka take Mace An rabaki da rashin lafiyar ki Duba, duba ta warke, abin mamaki abin al'ajabi, kuzo ku gani Ɗaukaka Ga Allah Shekaru sha takwas Allah ya saka maka Malam Akwai ranaku shida don yin aiki Kuzo mana a warkar da ku a ranakun Amma ba'a ranar asabar ba Munahikai Ashe kowannen ku baya kwance saniyar sa ko jakin shi ya kaishi ban ruwa ranar asabar Matannan ƴar zuriyar Ibrahim wadda sheɗan ya daure ta yau shekara goma sha takwas Ba sai a kwance ta ko ran asabar ba Malam managarci Me zanyi domin na gaji rai ma dauwami Don me ka ƙira ni managarci? Ai managarci sai Allah kaɗai Kasan waɗannan dokokin bazakai zina ba Kada kayi kisan kai Kada kayi shaidar zur Ka bada girma ga iyayen ka Ai na kiyaye duk waɗannan dokoki tun ƙuruciya ta Har yanzu abu gada ne ya rage maka Ka sayar da duk mallakarka ka rabama gajiyayyu Zaka samu wadata a sama Sa'annan kazo ka bini Mu fatake ne Attajirai Daker nefa masu dukiya su shiga mulkin Allah Ai zai fiyewa rakumi yabi ta ramin allura Da mai arziki ya shiga mulkin Allah Wa zai samu ceto kenan? Ai abinda yafi ƙarfin mutum zaiyiwu a wurin Allah A ina wannan zai kasance Mulkin Allah? Ai bayyanan mulkin Allah ba ganin sa ake da ido ba Ba wanda zaice Duba Gashi nan ko gashi can a'a Mulkin Allah a tsakanin ku yake Lokaci zaizo da za'a fiso ganin rana daya daga cikin ranakun dan mutum Amma baza ku gani ba Kamar yadda walkiya takeyi A bangon duniya haka ɗan mutum zai zama a ranar bayyanarsa Amman sai yasha wahala tukunna mutanen zamaninnan su kuma ƙi shi tukunna Zaifi sauki sararin sama da ƙasa su shude da digo daya na attaura ya gushe Annabawa da sarakuna na son ganin abinda kuka gani amma basu gani ba Suji abinda kuke ji amma basu ji ba Toh me zamuyi? Me nasin yace Ya ya kuke karantawa Ka kaunaci Ubangijinka Da dukkan zuciyarka Da dukkan ranka Da dukkan karfinka Da dukkan hankalin ka Ka kuma kaunaci makwabcinka [Daidai ne] kamar kanka Haka zaka rayu Wanene makwabcina? Ba dai sojojin nan ba To Kaisar fa? Wani mutum ya tashi daga Urshalima zashi Yariko yan fashi suka fada masa Suka dake shi har ya kusan mutuwa Wani firis ya biyo ta wannan hanya Da ya ganshi Ya zaga ya wuce Haka ma wani Balewe Ya iso wurin ya ganshi Shima ya zaga ta ɗaya gefe ya wuce Ana nan sai hanya ta kawo wani Basamariye inda yake Da yagan shi sai tausayi ya kamashi Yaje wurin sa Ya zuba masa mai da ruwan inabi Sa'annan ya ɗora shi akan dabbar sa yayi ta jinyar sa Washegari ya ɗebi kuɗi ya ba megidan yayi jinyarsa Duk kuma abinda ka kashe Bayan wannan Sai in biya ka Cikin ukun nan Wa kake tsammani ya zama ɗan'uwa ga wanda ƴan fashi suka faɗa masa? Wanda ya nuna masa jinƙai Ku ma kuyi haka Aha Kubar yara ƙanana suzo guna kada ku hanasu Ai mulkin Allah na irin sune Haƙiƙan ina gaya maku Duk wanda baiyi na'am da mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, bazai shiga mulkin ba Wanda ya marabci yaro a cikin sunana ya marabceni Wanda ya marabceni ya marabci wanda ya aikoni Wanda yake ƙarami a cikin ku shi ne mai girma Kai meke faruwa, me akeyi? Yesu Kiriti Banazare ne yake wucewa Yesu! Yesu Yesu ɗan Dauda Yi mini jin ƙai Me kake so inyi maka? In samu ganin gari Karɓi warkarwa Ban gaskiyarka ta warkar da kai Ina gani Na iya gani Ina gani Yesu kama hanya zuwa Urshalima jama'a suka bishi Suna tambaya yadda zasu samu ceto Yesu ya yi musu koyarwa gameda mulkin Allah Lallai mutumin nan annabi ne Ya Ubangiji ka cece ni Ubangiji ka cecemu Yabi Ubangiji Nuna mana hanyar gaskiya Ubangiji Mutane su soma yarda da Yesu cewa shine Ubangiji A Yariƙo akwai wani mutum mai suna Zakka Ya nemi ganin Yesu harya hau wani durumi [Ina mai karɓan haraji] domin ya ganshi Zakka maza ka sauƙo Domin yau a gidanka zan sauƙa A gida na Wa zai so ya sauƙa a gidan sa Ta yaya Zakka ya san Yesu? Kuji Zan bada Rabin mallakata Wa gajiyayyu Kowa na Zalunta kuwa Zan mayar masa Da ninki huɗu Ban gaskantaba Mai karɓan haraji ya mayar da kuɗi Basi yiwuwa Yau kam ceto yasauko a gidannan Tunda yake mutumin nan ma ɗan zuriyar annabi Ibrahim ne Ɗan mutum yazo neman abin da ya ɓata Kuji Zamu Urshalima abin da ke rubuce game da ɗan mutum zai tabbata Gama za'a basheshi ga al'ummai Kuyi masa ba'a A wulaƙantashi a kuma tofa masa miyau Su bulaleshi, su kashe shi Amma ranar Ta uku zai tashi Yesu ya san cewa za'a kashe shi domin zunuban ƴan Adam Amma yayi gaba zuwa Urshalima Mutane da yawa sukai murna, sukace da shi sarkinsu Malam Kwaɓi almajiran ka suyi shiru Koda almajiraina sun yi shiru Duwatsunnan ma sai su ɗauki sowa Ranka yadade Da Yesu ya hangi Urshalima yayi juyayin birnin da mazaunan sa Dama ace Kunsan hanyoyin da ke kawo salama yanzu boye suke gareku Raneku na zuwa da mikiyan ku zasu muku kawanya suyi maku zobe su matseku ta kowani gefe Tsakanin nan ne zasu halaku Kuda ƴaƴan ku Baza subar wani dutse akan wani a birninku ba don basu gane irin alherin da an sauƙar maku ba Haikalin dake Urshalima ya zamo wurin ciniki maimakon gidan sujada Ɗaya, biyu, uku, hudu, biyar, shida, bakwai, takwas, tara, goma, sha ɗaya, sha biyu, sha uku, sha hudu, sha biyar, sha shida, sha bakwai, sha takwas, sha tara, ashirin, ashirin da daya, ashirin da biyu A rubuce yake Gidana zaya zama gidan addu'a Amma ku kun maishe shi kogon mafasa Dubi Ya nufi dabbobina Tsare shi Tsare shi A kira ƴan tsaro A kira ƴan tsaro Gardama ta tashi tsakanin wasu shugabannin siyasa da na addini Don mutane nacewa Yesu sarkine Nagane cewa mutane na ɗaukaka shi kamar sarki Sarki Sarkin maroƙa, karuwai da ɓarayi Munsha ganin irinsu Zasu zo su sheƙa ayarsu su tafi A manta da su Karka ruɗe Mabiyansa ƙaruwa sukeyi kullum Yana da farin jini garesu Cewa shi sarki ne Toh bari in gargarɗe ku In mutumin nan ya cigaba da tada husuma Kune zan hukunta Gaskiya nefa Yakamata mu tuhumeshi Sa'adda sashin ƴan riya da Farisiyawa suke ƙara tsanantawa Yesu Farisiyawa masu binsa cikin Yahudawa na ƙaruwa Haka kuma masu gaba da shi waɗanda ya kayar Ɗan kadan ne A hailkali Yesu yaga wata gauruwa ta saka anini biyu cikin tasa Baki ƙarawa? Ina gaya maku Abinda gwauron nan tasaka yafi na kowa Domin waɗannan duka Sun bayar daga yalwar su ne Cikin rashinta ta bada dukkan mallakanta Gayamana Da wani izini kake faɗin abubuwannan Wa yaba ka izinin? Nima zanyi maku tambaya Wai babtismar Yahaya Ta Allah ce ko ta mutum ce? To me zamu ce In munce daga sama take Zaice to don me Bamu gaskanta da shi ba In munce ta mutum ce sai jama'a su jejjefe mu Don sun tabbata Yahaya annbi ne Bamu san inda ya fito ba Bazan faɗa maku koda wani izini nake aiki ba Wani mutum ne yayi gonar inabi Yaba manoma aronta Ya tafi wata ƙasa ya daɗe Da amfanin gonar isa girbi Ya aiki bawansa gun manoma Domin su bashi nashi rabo daga gonar Manoman sukai masa duka ya koma hannu wofi Sai ya aiki wani bawa Shima sun masa duka Suka walaƙanta shi suka koreshi hannu wofi Sai ya aiki na uku shima sunyi masa rauni Suka koreshi sai mai gonar yacema kansa Me zanyi kenan? Zan aiki ƙaunataccen ɗana Haƙikan zasu bashi girma Amma da manoman suka ganshi sai sukace ga junansu Ai wannan shine magajin Mu kashe shi sai gadon ya zama namu Ka cigaba Sai suka fidda shi daga gonar Suka kashe shi Me kuke zaton ubangijin nan zaiyi da manoman Zaizo ya hallaka mugayen manoman nan ya ba wani gonar Menene nasin nan ke faɗi? Dutsin da magina suka ƙi shi ne ya zama Dutsi nafi muhimmanci na gini Dukkan wanda ya faɗa akan dutsin nan sai ya ragargaje Amma wanda dutsin ya faɗawa Niƙe shi zaiyi kamar gari Malam Mun san cewa koyarwarka gaskiya ce Ka ɗauki kowa dai-dai babu banbanci sai dai koyar da tafarkin Allah dai dai ka keyi Gayamana Dai-dai ne bisa ga shari'a mu biya haraji ga mai mulkin Roma Ko kuwa? Ubangiji yi hankali da su dai Fito da kuɗin mugani Hoton wa da sunan wa kega kuɗin Kaisar To sai kuba Kaisar Abinda kena Kaisar Kuba Allah Abinda kena Allah To yanzu me zakuce? Bukin gurasa mara yisti wanda ake ƙira idin ketarewa ya kusa Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya domin su shirya idin ƙetarewa Naso cin abincin idin ƙetarewa daku ƙwarai kafin in sha wuya Ina gaya maku Bazan ƙara cinsa ba sai an bada cikakkiyar ma'anarsa a mulkin Allah Mai albarka ne kai Allan mu Sarkin halitta Mai bada abin sha daga ƴaƴan itace Karɓi wannan ku raba tsakanin ku Ina gaya maku bazan ƙara shan ruwan inabin ba sai mulkin Allah ya bayyana Mai albarka ne kai ya Allan mu Sarkin halitta Wanda yake kawo abinci daga ƙasa Wannan jikina ne da za'a bayar domin ku Ku riƙa yin haka don tunawa da ni Ƙoƙon sabon alkawali ne daga jinina da an zubar domin ku Gashi mai basheni ɗin nan yana ci a akwashi ɗaya tare da ni Lallai ɗan mutum zai ƙaura kamar yadda an kaddara amma kaiton mutuminnan mai bashe shi Ko nine? Tambaye shi wanne yake nufi Ubangiji! Wane ne? Wanene munafukin ya Ubangiji? Babba acikin ku ya zama kamar ƙarami Shugaba ya zama kamar mai hidima Wa yafi girma? Wanda ya zauna cin abinci ko mai hidimar? Wanda ya zauna mana Gashi ina cikin ku kamar mai hidima Tare muke cikin wahaluna Kamar wadda ubana ya bani mulkin Haka ni nake baku ikon Zaku ci ku sha tare da ni a mulkina Zaku zauna a kursiyay ku mulki ƙabibun Isra'ila sha biyun Ashe ba munafikin ma Siman Siman kaji Sheɗan ya nemi izini ya gwada ku Ya sheƙe ku kamar yadda manomi ya ke sheƙe alkamar sa Nayi addu'a kada bangaskiyarka ta kasa Siman Bayan ka juyo wuri na ka ƙarfafa ƴan'uwan ka Ubangiji ina shirye in bika har kurkuku Har ma mu mutu tare Haƙiƙa Bitrus yauma kafin charar zakara zakai musun sanina sau uku Da na aikeku ba kuɗi ba jikka akwai abunda kuka rasa Babu. Ko kaɗan Amma yanzu duk mai kuɗi ko jikka ya ɗauka Wanda bashida komai ya saida mayafinshi ya saya Ina gaya maku A rubuce yake cewa an lisafta shi cikin masu laifi Abinda an faɗa a kaina ya tabbata Duba Ga takuba biyu Ubangiji To ya isa Sai shugabannin sukayi shawara akan yadda zasu kashe Yesu Sai sheɗan ya shiga Yahuza dan Iskariyoti daya daga cikin sha biyun Ya gama baki da shugabannin don kama Yesu Yesu yabar Urshalima zuwa dutsen zaitun don yin addu'a Kuyi addu'a don kada ku faɗa ga gwaji Yahudu Iskariyoti ya sayar da Yesu kan kuɗi azurfa talatin Yasan lokacin mutuwarsa don zunuban ƴan adam yayi sai yayi addu'a Ya uba Indai ka yarda Ka ɗauke mini wahalan nan Duk da haka Ba nufina zaɓi ba sai dai naka Mala'ika ya bayyana gareshi don ƙarfafa shi Har jikinsa na ɗiɗɗiga kamar manyan ɗiɗɗigar jini Don me kuke barci Ku tashi Kuyi addu'a kada ku shiga cikin jaraba Yahuda Da sumba ne kake son ka bada ɗan mutum Ubangiji mu sara da takobi ne? Ku kama shi Ya isa haka Abun al'ajabi Kunzo da tokubba da kulake kamar masu kama dan fashi Da nake tare daku cikin Haikali baku kamani ba Amma wannan zarafin kune Dana mulkin duhu kuma Ku kamashi Tare shi da kyau Sojojin suka kaishi cikin fada sukayi ta masa ba'a Ga rigar da sarki yasa Yi anabci me zai faru Zaka cecemu ko ranka shi daɗe ai zaka cecemu Mutumin nan na tare da Yesu Ke Ni banma san shi ba Na gansu tare Gamunan talakawan ka Yaya ka kaji yanzu a hannun wani Kaima tare da su kake A'a bana cikin su Ba shakka mutumin na tare da Yesu don shima Bagaliline Gafara nan Nifa bansan Abinda kake cewa ba Sai Yesu ya juya ya dubi Bitrus Bitrus kuwa ya tuna da abinda Ubangiji yace Yau kafin charar zakara zaka yi musun sani na sau uku Ya Ubangiji nayi maka laifi ka gafarta mani na roƙe ka ka gafarta mini laifina Ubangiji Mai jinƙai Kayimini jinƙai Naga kasawata a gabanka Ya mai jinƙai Mai jin kukan masu laifi Kaji kukana da roƙona Na tuba Na tuba Ka yafe mini Bazan ƙaraba kuma ba Saboda jinƙan ka Ina rokon ka Ina rokon ka gafara Wa ya bugeka Yi annabci Wazai sake bugunka Ku bari! Ku bari nace Ku kawoshi yanzu gaban majalisa Muje! Ƴan majalisa sun taru don suyiwa Yesu shari'a Gaya mana Kai ne Almasihu? Ko na gaya maku Baza ku gaskantani ba In nayi tambaya Bazaku bani amsa ba Amma nan gaba ɗan mutum zai zauna a hannun dama na Allah mai iko duka Wato Kai ɗan Allah ne? Kun faɗa nine Saboda me zai faɗi haka wa ya bashi ikon faɗar haka, ina ya samu ikon fadar haka? Oho An tabbatar da laifin sa Muma munji abunda yace Zamu kai shi gaban Bilatus ku tafi da shi kaishi wurin Bilatus shi zai hukuntashi Yi gaba Suka kai shi gaban sarki Bilatus wanda yafi dukkan sauran gwamnoni mugunta Shi kaɗai ya giciye dubban mutane Shin me kuke so anan Da sassafe haka Mun samu mutumin nan yana ɓadda jama'an mu Ya tada hankalin jama'a a majami'a Wani hukunci za ayi masa? A hukunta shi Ban iske mutumin da wani laifi ba Babu dalili Mun sameshi da laifi Yana hana a biyawa Kaisar haraji Yace shine almasihu Sarki Sarki? Kai ne sarkin Yahudawa? Haka ku ka ce Ya faro a Galili Yanzu gashi yazo nan A Galili Mutumin Bagalili ne? In haka ne Hirdus ya shar'anta shi Yana nan a Galili ko kuwa bashi Kai shi wurin Hirdus Wanene kai Mai ka ƙira kanka Su waɗanne ne ka ke ce da su almajiran ka? Mutane da yawa sunce kana iya aikin al'ajabi Kayi mini In gani Ya mai girma Mutumin nan na ɓadda jama'ar mu Ya ce da kansa Sarki Wannan mutum? Sarki? Ranka ya dade Buge shi sosai Komar dashi gun Bilatus Wannan yankin ƙasar suce Wannan mutum baiyi laifin da ya isa mutuwa ba Saboda haka mayi masa bulala Sa'annan a sake shi Muna so a sakar mana da daurarre guda a lokacin idin nan Sakar mana Barabas Ea Barabas Tafi da mutumin nan Ea sakar mana Barabas A gicciye shi Ea A giciye shi Kai Kai kuyi masa bulala Sarki Bilatus Me ka ke jira Yesu ne Me yasa kuke wahal da shi? Wai shi ɗan Allah ne Kubar shi shine Almasihu Baiyi komai ba Ku ɗaga shi Mutane suka yita ihu da karfi suna cewa a giciye shi Bilatus ya yankewa Yesu hukuncin kisa Ya sakar musu da Barabas da aka jefa a kurkuku kan laifin tawaye da kuma kisan kai ya bada Yesu a giciye Baya koma baya , baya, baya can, matsa daga gun sa Ja baya Ja baya Baya Sarari Bada wuri Fita Kai bada wuri Tafi ina gaya maka Tashi tsaye, tashi tsaye Kai Ya sunan ka? Saminu Bakurani Zo kusa nan Yanke igiyar Ka sauƙe shi Muje gaba Baya Baya Barshi Yi gaba Ku bada wuri can Koma baya Koma baya Munyi kuka domin ka Ubangiji Sha wannan Sha Sha Ubangiji Matan Urshalima kubar yi mini kuka Kuyi kuka don kanku da kuma ƴaƴan ku in abubuwa irin wadannan zasu iya faruwa da danyen itace Mai zai faru in ya bushe? Allah ya taimake ka Zamu yi maka addu'a Tafi Ƙasa nan Bini Maza Maza Kai tafi Muje Bisu maza Bini Maza Yanzu tafi Tafi Yanzu kai yi gaba Bini yanzu Cigaba da shi Ɗaga Kai baka ƙusar Cire igiyar Uba ka gafarce su Don basu san abunda suke yiba Ya ceci waɗansu Ya ceci kansa mana Yauwa Ceci kanka in kai Almasihu ne Sauƙo daga giciyen Nuna aikin ka da mujiza Aka giciye Yesu tsakanin barayi biyu don a cika annabci yadda annabawa suka fada a shekarun baya Ku gani wannan ba rigar banza bace Aka sa alama kan giciyen cewa shi ne sarkin Yahudawa Ceci kanka in kaine sarkin Yahudawa Ba Kaine Almasihu ba Ceci Kan ka Da mu mana Ko Tsoron Allah Baka ji Mun karɓi Hukunci Dai-dai da shi Naka Dai-dai ne Amma mutumin Baiyi laifi Ka tuna da ni ya Yesu Sa'adda ka shiga Mulkin ka Ina gaya maka Yau zaka kasance a aljanna Tare da ni To da tsakar rana ne kuwa sai duhu ya rufe kasar har karfe uku na yamma Labulen cikin Haikalin ya tsage kashi biyu Ya uba Na mika ruhu A cikin Hannun ka Da jarumin ya ga abinda ya faru sai ya girmama Allah yace Alhamduka Allah Lallai mutumin nan mai adalci ne Yusufu mutumin Armatiya ɗan majalisa ne kuma adali Bai yarda da hukuncin da akayi ba yaje wurin Bilatus ya roƙa a bashi gawar Yesu yasa a kabari kafin ranar sujada Ka yafemu Munzo gun gawar Ubangijin mune Ana marabtan kowa Kuyi sauri Ranar asabar na gabatowa A ranar farko ta mako da asussuba suka je kabarin da kayan Ƙamshin da suka shirya Sun tarar an mirgina dutsen a bakin kabarin sun shiga basu samu gawar Yesu ba Ayy ya tashi Ku tuna ya gaya muku tun yana Galili cewa Lallai ne a bada ɗan mutum ga hannuwan mutane masu zunubi A giciye shi Rana ta uku kuma Ya tashi da rai Kuji An mirgina dutsen Mun shiga Mun tarar gawan Ubangiji Bata Nan Mene? Babu gawar Ubangiji Sai mutum biyu suka bayyana Mala'iku na haske Kamar rana Suka ce mana Don me kuke neman mai rai Cikin matattu Gaskiya ne Gaskiya ne Ba ƙarya ba Mun gansu Kuje ku gani ba Yesu a kabarin Ta tashi Bitrus Gaskiya ne Yesu ya bayyana ga biyu daga cikin almajiran da murna suka komo gun saura Lallai Ubangiji ya tashi Harya bayyana ga Sima Bamu gane da shi ba Akan hanya Da ya gutsura gurasa Mun gane shi Imawus AbIn mamaki me ya kaishi Salamu'alaikum Don me kuka firgita? Don me kuke da shakka a zuciyar ku? Duba Hannuwa na da ƙafafuwa na Taɓa ni mana Ay nine Ay nine da kai na Ay fatalwa bata da tsoka da ƙashi kaman yadda nake dasu Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare Lallai ne a cika abinda ka game da ni a attaura ta Musa littattafan annabawa da zabura Haka yake a rubuce Lallai ne Almasihu yasha wuya A rana ta uku ya tashi da rai A kuma yiwa Al'ummai wa'azi su tuba a gafarta musu zunuban su saboda sunan sa Za'a fara daga Urshalima Kune shaidun waɗannan abubuwa Gashi na kawo muku abunda ubana ya alkawarta Ku dakata a birni tukuna Har ayi muku baiwar iko daga sama Allah ya albarkace ku ya tsare ku An mallaka mani iko a sama da ƙasa Kuje ku koyawa al'ummai Kuna musu babtisma da sunan Uba da Ɗa dana Ruhu Maitsarki Kuna koya masu Su kiyaye abinda na umurce ku Gashi ni kuma kullum ina tare da ku har ƙarshen zamani Ameen Cikin littafi mai tsarki Allah ya shaida Almasihu zaizo ya ceci dukkan duniya Rayuwar Yesu ta shaida lallai shi ne annabawa suka yi zancen zuwan sa Annabi Ishaya yace wata budurwa zata yi ciki ta haifi ɗa Bayan shekaru da dama haihuwar Yesu ta cika wannan annabcin Littafi mai tsarki yace mai tsarkin nan da za'a haifa za'ace da shi ɗan Allah Wato za'a kira Yesu ɗan Allah ba ɗa na jikiba amma ɗa na ruhu Hakan ya bayyana ta wurin rayuwarsa Ya warkar da masu cuta Ya gafarta zunubansu ya shirya su da Allah Ya kuma alƙawarta musu mulkin Allah na har abada Ya bada kansa hadaya domin zunuban su ya tashi daga matattu Yesu yace ba me karɓe mini rai don kaina nake bada shi Rayuwar Yesu ta cika annabcin annabawa ta kuma ƙarfafa gaskiyar maganar Allah Annabawa sun shaida cewa Maganar abar dogara ce kuma tabbatacciya ce ya Ubangiji Yesu yace sama da ƙasa zasu shuɗe amma maganata bazata shuɗe ba Yesu ya zo ya bamu rai a yalwace Ganin yadda mutum ya yiwa Allah rashin biyayya a gonar adinin Mutum ya zaɓi bin hanyar sa wacce ta rabasa da mahaliccin sa Littafi mai tsarki yace Ƴan Adam duka sunyi zunubi Sakamakon zunubi kuma mutuwa ne Wato mutuwa ta ruhu kenan Kamar yadda Allah ya tanada rago a maimakon ɗan Ibrahim Haka Allah ya aiko Almasihu ya mutu a madadin mu Rayuwa da mutuwa da tashin sa sun mai da dangantaka tsakanin Allah da masu dogara ga Yesu Yanzu masu bin Yesu ba gafarta zunuban su kaɗai akayi ba Amma an cecesu daga hukunci An tabbatar musu da shiga aljanna Rai da yanci daga ikon zunubi ne Yesu keba kowa a yau Ba bin wani addini ba amma ana zancen gaskata Yesu wanda yace Ganinan tsaye a bakin kofa ina ƙwanƙwasawa Kowa yaji murya ta ya bude kofar sai in shiga wurin sa Ana nufin mu juyo ga Allah mu dogara ga Yesu ya shigo zukatan mu Ya gafarta mana ya maishe mu karɓaɓɓu gareshi ba abin marmari ko tunanin sa a zuciya kaɗai ba Karɓarsa zamu yi da son ran mu ta wurin alheri saboda ban gaskiya Duk wanda keso yazamo mai bin Yesu Almasihu zai iya magana da shi cikin addu'a Mai yuwa kana shirye ka buɗe kofar zuciyar ka zaka iya yin wannan addu'ar a cikin zuciyar ka Ya Yesu Ina bukatarka Nagode da mutuwar da kayi don zunubai na Na furta zunubai na da roƙon gafara Na buɗe zuciyata na karɓe ka kazamo mai ceto na da Ubangiji na Nagode domin gafarar zunubai na domin ka bani rai na har abada Ka maishe ni irin mutumin da ka keso Yanzu da na zamo cikin masu binka Ameen Yesu yayi magana kan masu binsa da cewa Tumaki na sun san murya ta na sansu suna bina In masu bin Yesu suna so su samu rai da ya alkawarta Dole ne suyi addu'a suna karatu da sauraran maganar Allah kullum Suyi ta zumunci da juna suna shaida shi ga wasu Tuna da alƙawarin sa Cewa an mallaka mini iko dukkan sama da ƙasa Gashi ni kuma ina tare da ku har matuƙar zamani
JesusFilm